Suratul Kahf
Kogo (Alƙur'ani 18), don ranar Juma'a
“Wanda ya karanta Suratul Kahf a ranar Juma'a, haske zai haskaka masa tsakanin Juma'a biyu.”
-
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
Bismillahir rahmanir rahim
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
-
الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَنزَلَ عَلَىٰ عَبْدِهِ الْكِتَابَ وَلَمْ يَجْعَل لَّهُ عِوَجًا ۜ ١
Al hamdu lillahil lazi anzala 'ala 'abdihil kitaba wa lam yaj'al lahu 'iwaja
Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya saukar da Littafi a kan bãwansa kuma bai sanya karkata ba a gare shi.
-
قَيِّمًا لِّيُنذِرَ بَأْسًا شَدِيدًا مِّن لَّدُنْهُ وَيُبَشِّرَ الْمُؤْمِنِينَ الَّذِينَ يَعْمَلُونَ الصَّالِحَاتِ أَنَّ لَهُمْ أَجْرًا حَسَنًا ٢
Qayyimal li yunzira ba'san shadidam mil ladunhu wa yubashshiral mu'mininal lazina ya'malunas salihati anna lahum ajran hasana
Madaidaici, dõmin Ya yi gargaɗi da azãba mai tsanani daga gare shi, kuma Ya yi bushãra ga mũminai, waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai da (cẽwa) sunã da wata lãdã mai kyau.
-
مَّاكِثِينَ فِيهِ أَبَدًا ٣
Makisina fihi abada
Sunã mãsu zama a cikinta har abada.
-
وَيُنذِرَ الَّذِينَ قَالُوا اتَّخَذَ اللَّهُ وَلَدًا ٤
Wa yunziral lazina qaluttakhazallahu walada
Kuma Ya yi gargaɗi ga waɗanda suka ce: "Allah yanã da ɗa."
-
مَّا لَهُم بِهِ مِنْ عِلْمٍ وَلَا لِآبَائِهِمْ ۚ كَبُرَتْ كَلِمَةً تَخْرُجُ مِنْ أَفْوَاهِهِمْ ۚ إِن يَقُولُونَ إِلَّا كَذِبًا ٥
Ma lahum bihi min 'ilmin wa la li aba'ihim kaburat kalimatan takhruju min afwahihim in yaquluna illa kaziba
Ba su da wani ilmi game da wannan magana, kuma iyãyensu bã su da shi, abin da ke fita daga bãkunansu ya girma ga ya zama kalmar faɗa! Ba su faɗan kõme fãce ƙarya.
-
فَلَعَلَّكَ بَاخِعٌ نَّفْسَكَ عَلَىٰ آثَارِهِمْ إِن لَّمْ يُؤْمِنُوا بِهَٰذَا الْحَدِيثِ أَسَفًا ٦
Fa la'allaka bakhi'un nafsaka 'ala asarihim il lam yu'minu bi hazal hadisi asafa
To, kã yi kusa ka halaka ranka a gurabbansu, wai dõmin ba su yi ĩmãni da wannan lãbãri ba sabõda baƙin ciki.
-
إِنَّا جَعَلْنَا مَا عَلَى الْأَرْضِ زِينَةً لَّهَا لِنَبْلُوَهُمْ أَيُّهُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا ٧
Inna ja'alna ma 'alal ardi zinatal laha li nabluwahum ayyuhum ahsanu 'amala
Lalle ne Mũ, Mun sanya abin da ke kan ƙasa wata ƙawa ce gare ta, dõmin Mu jarraba su; wanne daga cikinsu zai zama mafi kyau ga aiki.
-
وَإِنَّا لَجَاعِلُونَ مَا عَلَيْهَا صَعِيدًا جُرُزًا ٨
Wa inna la ja'iluna ma 'alaiha sa'idan juruza
Kuma lalle Mũ, Mãsu sanya abin da ke a kanta (ya zama) turɓãya ƙeƙasasshiya ne.
-
أَمْ حَسِبْتَ أَنَّ أَصْحَابَ الْكَهْفِ وَالرَّقِيمِ كَانُوا مِنْ آيَاتِنَا عَجَبًا ٩
Am hasibta anna ashabal kahfi war raqimi kanu min ayatina 'ajaba
Ko kuwa kã yi zaton cẽwa ma'abũta kõgo da allo sun kasance abin mãmãki daga ãyõyin Allah?
-
إِذْ أَوَى الْفِتْيَةُ إِلَى الْكَهْفِ فَقَالُوا رَبَّنَا آتِنَا مِن لَّدُنكَ رَحْمَةً وَهَيِّئْ لَنَا مِنْ أَمْرِنَا رَشَدًا ١٠
Iz awal fityatu ilal kahfi fa qalu rabbana atina mil ladunka rahmatan wa hayyi' lana min amrina rashada
A lõkacin da samarin suka tattara zuwa ga kõgon, sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka bã mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka sauƙaƙe mana (sãmun) shiriya daga al'amarinmu."
-
فَضَرَبْنَا عَلَىٰ آذَانِهِمْ فِي الْكَهْفِ سِنِينَ عَدَدًا ١١
Fa darabna 'ala azanihim fil kahfi sinina 'adada
Sai Muka yi dũka a kan kunnunwansu, a cikin kõgon, shẽkaru mãsu yawa.
-
ثُمَّ بَعَثْنَاهُمْ لِنَعْلَمَ أَيُّ الْحِزْبَيْنِ أَحْصَىٰ لِمَا لَبِثُوا أَمَدًا ١٢
Summa ba'asnahum li na'lama ayyul hizbaini ahsa lima labisu amada
Sa'an nan Muka tãyar da su, dõmin Mu san wane ɗayan ƙungiyõyin biyu suka fi lissãfi ga abin da suka zauna na lõkacin.
-
نَّحْنُ نَقُصُّ عَلَيْكَ نَبَأَهُم بِالْحَقِّ ۚ إِنَّهُمْ فِتْيَةٌ آمَنُوا بِرَبِّهِمْ وَزِدْنَاهُمْ هُدًى ١٣
Nahnu naqussu 'alaika naba'ahum bil haqqi innahum fityatun amanu bi rabbihim wa zidnahum huda
Mu ne ke jẽranta maka lãbãrinsu da gaskiya. Lalle ne sũ, waɗansu samãri ne. Sun yi ĩmãni da Ubangijinsu, kuma Muka ƙãra musu wata shiriya.
-
وَرَبَطْنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ إِذْ قَامُوا فَقَالُوا رَبُّنَا رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ لَن نَّدْعُوَ مِن دُونِهِ إِلَٰهًا ۖ لَّقَدْ قُلْنَا إِذًا شَطَطًا ١٤
Wa rabatna 'ala qulubihim iz qamu fa qalu rabbuna rabbus samawati wal ardi lan nad'uwa min dunihi ilahal laqad qulna izan shatata
Kuma Muka ɗaure a kan zukãtansu, a lõkacin da suka tsayu, sa'an nan suka ce: "Ubangijinmu Shĩ ne Ubangijin sammai daƙasa. Bã zã mu kirãyi wanin Sa abin bautawa ba. (Idan mun yi haka) lalle ne, haƙĩƙa, mun faɗi abin da ya ƙẽtare haddi a sa'an nan."
-
هَٰؤُلَاءِ قَوْمُنَا اتَّخَذُوا مِن دُونِهِ آلِهَةً ۖ لَّوْلَا يَأْتُونَ عَلَيْهِم بِسُلْطَانٍ بَيِّنٍ ۖ فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَىٰ عَلَى اللَّهِ كَذِبًا ١٥
Ha'ula'i qaumunattakhazu min dunihi alihatal laula ya'tuna 'alaihim bi sultanin bayyinin fa man azlamu mimmaniftara 'alallahi kaziba
"Ga waɗannan mutãnenmu sun riƙi waninSa abin bautãwa! Don me bã su zuwa da wata hujja bayyananna a kansu (waɗanda ake bautawar)? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙãga ƙarya ga Allah?"
-
وَإِذِ اعْتَزَلْتُمُوهُمْ وَمَا يَعْبُدُونَ إِلَّا اللَّهَ فَأْوُوا إِلَى الْكَهْفِ يَنشُرْ لَكُمْ رَبُّكُم مِّن رَّحْمَتِهِ وَيُهَيِّئْ لَكُم مِّنْ أَمْرِكُم مِّرْفَقًا ١٦
Wa izi'tazaltumuhum wa ma ya'buduna illallaha fa'wu ilal kahfi yanshur lakum rabbukum mir rahmatihi wa yuhayyi' lakum min amrikum mirfaqa
"Kuma idan kun nĩsance su sũ da abin da suke bautãwa, fãce Allah, to, ku tattara zuwa ga kõgon sai Ubangijinku Ya watsa muku daga rahamar Sa kuma Ya sauƙaƙe muku madõgara daga al'amarinku."
-
وَتَرَى الشَّمْسَ إِذَا طَلَعَت تَّزَاوَرُ عَن كَهْفِهِمْ ذَاتَ الْيَمِينِ وَإِذَا غَرَبَت تَّقْرِضُهُمْ ذَاتَ الشِّمَالِ وَهُمْ فِي فَجْوَةٍ مِّنْهُ ۚ
Wa tarash shamsa iza tala'at tazawaru 'an kahfihim zatal yamini wa iza gharabat taqriduhum zatash shimali wa hum fi fajwatim minh
Kuma kanã ganin rãnã idan ta fito tanã karkata daga kõgonsu wajen dãma kuma idan ta fãɗi tanã gurgura su wajen hagu, kuma su, sunã a cikin wani fili daga gare shi.
-
ذَٰلِكَ مِنْ آيَاتِ اللَّهِ ۗ مَن يَهْدِ اللَّهُ فَهُوَ الْمُهْتَدِ ۖ
Zalika min ayatillahi man yahdillahu fa huwal muhtad
Wannan abu yanã daga ãyõyin Allah. Wanda Allah Ya shiryar, to shĩ ne mai shiryuwa,
-
وَمَن يُضْلِلْ فَلَن تَجِدَ لَهُ وَلِيًّا مُّرْشِدًا ١٧
Wa man yudlil fa lan tajida lahu waliyyam murshida
kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmar masa wani majiɓinci mai shiryarwa ba.
-
وَتَحْسَبُهُمْ أَيْقَاظًا وَهُمْ رُقُودٌ ۚ وَنُقَلِّبُهُمْ ذَاتَ الْيَمِينِ وَذَاتَ الشِّمَالِ ۖ
Wa tahsabuhum aiqazan wa hum ruqudun wa nuqallibuhum zatal yamini wa zatash shimal
Kuma kanã zaton su farkakku ne, alhãli kuwa sũ mãsu barci ne. Munã jũya su wajen dãma da wajen hagu,
-
وَكَلْبُهُم بَاسِطٌ ذِرَاعَيْهِ بِالْوَصِيدِ ۚ لَوِ اطَّلَعْتَ عَلَيْهِمْ لَوَلَّيْتَ مِنْهُمْ فِرَارًا وَلَمُلِئْتَ مِنْهُمْ رُعْبًا ١٨
Wa kalbuhum basitun zira'aihi bil wasidi lawittala'ta 'alaihim la wallaita minhum firaran wa la muli'ta minhum ru'ba
kuma karensu yanã shimfiɗe da zirã'õ'in ƙafãfuwansa ga farfãjiya (ta kõgon). Dã ka lẽka (a kan) su (dã) lalle ne, ka jũya daga gare su a guje kuma (dã) lalle ne ka cika da tsõro daga gare su.
-
وَكَذَٰلِكَ بَعَثْنَاهُمْ لِيَتَسَاءَلُوا بَيْنَهُمْ ۚ قَالَ قَائِلٌ مِّنْهُمْ كَمْ لَبِثْتُمْ ۖ
Wa kazalika ba'asnahum li yatasa'alu bainahum qala qa'ilum minhum kam labistum
Kuma kamar wannan ne Muka tãyar da su, dõmin su tambayi jũna a tsakãninsu. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Mẽne ne lõkacin da kuka zauna?"
-
قَالُوا لَبِثْنَا يَوْمًا أَوْ بَعْضَ يَوْمٍ ۚ
Qalu labisna yauman au ba'da yaum
suka ce: "Mun zauna yini ɗaya ko sãshen yini."
-
قَالُوا رَبُّكُمْ أَعْلَمُ بِمَا لَبِثْتُمْ فَابْعَثُوا أَحَدَكُم بِوَرِقِكُمْ هَٰذِهِ إِلَى الْمَدِينَةِ فَلْيَنظُرْ أَيُّهَا أَزْكَىٰ طَعَامًا فَلْيَأْتِكُم بِرِزْقٍ مِّنْهُ وَلْيَتَلَطَّفْ وَلَا يُشْعِرَنَّ بِكُمْ أَحَدًا ١٩
Qalu rabbukum a'lamu bima labistum fab'asu ahadakum bi wariqikum hazihi ilal madinati falyanzur ayyuha azka ta'aman falya'tikum bi rizqim minhu walyatalattaf wa la yush'iranna bikum ahada
Suka ce: "Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da kuka zauna. To, ku aika da ɗayanku, game da azurfarku wannan, zuwa ga birnin. Sai ya dũba wanne ne mafi tsarki ga abin dafãwa, sai ya zo muku da abinci daga gare shi. Kuma sai ya yi da hankali, kada ya sanar da ku ga wani mutum."
-
إِنَّهُمْ إِن يَظْهَرُوا عَلَيْكُمْ يَرْجُمُوكُمْ أَوْ يُعِيدُوكُمْ فِي مِلَّتِهِمْ وَلَن تُفْلِحُوا إِذًا أَبَدًا ٢٠
Innahum in yazharu 'alaikum yarjumukum au yu'idukum fi millatihim wa lan tuflihu izan abada
"Lalle ne sũ idan sun kãmã ku, zã su jẽfẽ ku, kõ kuwa su mayar da ku a cikin addininsu kuma bã zã ku sãmi babban rabo, ba, a sa'an nan har abada."
-
وَكَذَٰلِكَ أَعْثَرْنَا عَلَيْهِمْ لِيَعْلَمُوا أَنَّ وَعْدَ اللَّهِ حَقٌّ وَأَنَّ السَّاعَةَ لَا رَيْبَ فِيهَا إِذْ يَتَنَازَعُونَ بَيْنَهُمْ أَمْرَهُمْ ۖ
Wa kazalika a'sarna 'alaihim li ya'lamu anna wa'dallahi haqqun wa annas sa'ata la raiba fiha iz yatanaza'una bainahum amrahum
Kuma kamar wancan ne, Muka nũna su (gare su) dõmin su san lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma lalle ne Sa'a bãbu shakka a cikinta. A lõkacin da suke jãyayyar al'amarinsu a tsakãninsu
-
فَقَالُوا ابْنُوا عَلَيْهِم بُنْيَانًا ۖ رَّبُّهُمْ أَعْلَمُ بِهِمْ ۚ
Fa qalubnu 'alaihim bunyanar rabbuhum a'lamu bihim
sai suka ce: "Ku gina wani gini a kansu, Ubangijinsu ne Mafi sani game da su."
-
قَالَ الَّذِينَ غَلَبُوا عَلَىٰ أَمْرِهِمْ لَنَتَّخِذَنَّ عَلَيْهِم مَّسْجِدًا ٢١
Qalal lazina ghalabu 'ala amrihim la nattakhizanna 'alaihim masjida
Waɗanda suka rinjãya a kan al'amarinsu suka ce: "Lalle mu riƙi masãllãci a kansu."
-
سَيَقُولُونَ ثَلَاثَةٌ رَّابِعُهُمْ كَلْبُهُمْ وَيَقُولُونَ خَمْسَةٌ سَادِسُهُمْ كَلْبُهُمْ رَجْمًا بِالْغَيْبِ ۖ وَيَقُولُونَ سَبْعَةٌ وَثَامِنُهُمْ كَلْبُهُمْ ۚ
Sa yaquluna salasatur rabi'uhum kalbuhum wa yaquluna khamsatun sadisuhum kalbuhum rajman bil ghaibi wa yaquluna sab'atun wa saminuhum kalbuhum
Zã su ce: "Uku ne da na huɗunsu karensu."Kuma sunã cẽwa, "Biyar ne da na shidansu karensu," a kan jĩfa a cikin duhu. Kuma sunã cẽwa, "Bakwaine da na takwas ɗinsu karensu."
-
قُل رَّبِّي أَعْلَمُ بِعِدَّتِهِم مَّا يَعْلَمُهُمْ إِلَّا قَلِيلٌ ۗ
Qur rabbi a'lamu bi 'iddatihim ma ya'lamuhum illa qalil
Ka ce: "Ubangijĩna ne Mafi saniga ƙidãyarsu, bãbu wanda ya san su fãce kaɗan."
-
فَلَا تُمَارِ فِيهِمْ إِلَّا مِرَاءً ظَاهِرًا وَلَا تَسْتَفْتِ فِيهِم مِّنْهُمْ أَحَدًا ٢٢
Fa la tumari fihim illa mira'an zahiran wa la tastafti fihim minhum ahada
Kada ka yi jãyayya bayyananna. Kuma kada ka yi fatawa ga kõwa daga gare su a cikin al'amarinsu.
-
وَلَا تَقُولَنَّ لِشَيْءٍ إِنِّي فَاعِلٌ ذَٰلِكَ غَدًا ٢٣
Wa la taqulanna li shai'in inni fa'ilun zalika ghada
Kuma kada lalle ka ce ga wani abu, "Lalle ni, mai aikatãwa ne ga wancan a gõbe."
-
إِلَّا أَن يَشَاءَ اللَّهُ ۚ وَاذْكُر رَّبَّكَ إِذَا نَسِيتَ وَقُلْ عَسَىٰ أَن يَهْدِيَنِ رَبِّي لِأَقْرَبَ مِنْ هَٰذَا رَشَدًا ٢٤
Illa an yasha'allahu wazkur rabbaka iza nasita wa qul 'asa an yahdiyani rabbi li aqraba min haza rashada
Fãce idan Allah Ya so. Kuma ka ambaci Ubangijinka idan ka manta, kuma ka ce: "¦ammãni ga Ubangijĩna, Ya shiryar da ni ga abin da yake shi ne mafi kusa ga wannan na shiriya."
-
وَلَبِثُوا فِي كَهْفِهِمْ ثَلَاثَ مِائَةٍ سِنِينَ وَازْدَادُوا تِسْعًا ٢٥
Wa labisu fi kahfihim salasa mi'atin sinina wazdadu tis'a
Kuma suka zauna a cikin kõgonsu shẽkaru ɗarĩ uku kuma suka daɗa tara.
-
قُلِ اللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا لَبِثُوا ۖ لَهُ غَيْبُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ
Qulillahu a'lamu bima labisu lahu ghaibus samawati wal ard
Ka ce: "Allah ne Mafi sani ga abin da suka zauna. Shĩ ne da (sanin) gaibin sammai da ƙasa.
-
أَبْصِرْ بِهِ وَأَسْمِعْ ۚ مَا لَهُم مِّن دُونِهِ مِن وَلِيٍّ وَلَا يُشْرِكُ فِي حُكْمِهِ أَحَدًا ٢٦
Absir bihi wa asmi' ma lahum min dunihi min waliyyin wa la yushriku fi hukmihi ahada
Mũne ne ya yi ganin Sa da jin Sa! Bã su da wani majiɓinci baicin Sa kuma bã Ya tãrayya da kõwa a cikin hukuncinsa."
-
وَاتْلُ مَا أُوحِيَ إِلَيْكَ مِن كِتَابِ رَبِّكَ ۖ لَا مُبَدِّلَ لِكَلِمَاتِهِ وَلَن تَجِدَ مِن دُونِهِ مُلْتَحَدًا ٢٧
Watlu ma uhiya ilaika min kitabi rabbika la mubaddila li kalimatihi wa lan tajida min dunihi multahada
Ka karanta abin da aka yi wahayi zuwa gare ka, na littãfin Ubangijinka. Bãbu mai musanyãwa ga kalmõminSa kuma bã zã kã sãmi wata madõgara ba daga waninsa.
-
وَاصْبِرْ نَفْسَكَ مَعَ الَّذِينَ يَدْعُونَ رَبَّهُم بِالْغَدَاةِ وَالْعَشِيِّ يُرِيدُونَ وَجْهَهُ ۖ
Wasbir nafsaka ma'al lazina yad'una rabbahum bil ghadati wal 'ashiyyi yuriduna wajhah
Ka haƙurtar da ranka tãre da waɗanda ke kiran Ubangijinsu, sãfe da maraice, sunã nufin yardar Sa.
-
وَلَا تَعْدُ عَيْنَاكَ عَنْهُمْ تُرِيدُ زِينَةَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۖ
Wa la ta'du 'ainaka 'anhum turidu zinatal hayatid dunya
Kuma kada idãnunka su jũya daga barinsu, kanã nufin ƙawar rãyuwar dũniya.
-
وَلَا تُطِعْ مَنْ أَغْفَلْنَا قَلْبَهُ عَن ذِكْرِنَا وَاتَّبَعَ هَوَاهُ وَكَانَ أَمْرُهُ فُرُطًا ٢٨
Wa la tuti' man aghfalna qalbahu 'an zikrina wattaba'a hawahu wa kana amruhu furuta
Kuma kada ka biwanda Muka shagaltar da zũciyarsa daga hukuncin Mu, kuma ya bi son zuciyarsa, alhãli kuwa al'amarinsa ya kasance yin ɓarna.
-
وَقُلِ الْحَقُّ مِن رَّبِّكُمْ ۖ فَمَن شَاءَ فَلْيُؤْمِن وَمَن شَاءَ فَلْيَكْفُرْ ۚ
Wa qulil haqqu mir rabbikum fa man sha'a falyu'min wa man sha'a falyakfur
Kuma ka ce: "Gaskiya daga Ubangijinku take." Sabõda haka wanda ya so, to, ya yi ĩmãni, kuma wanda ya so, to, ya kãfirta.
-
إِنَّا أَعْتَدْنَا لِلظَّالِمِينَ نَارًا أَحَاطَ بِهِمْ سُرَادِقُهَا ۚ
Inna a'tadna liz zalimina naran ahata bihim suradiquha
Lalle ne Mũ, Mun yi tattali dõmin azzãlumai wata wuta wadda shãmakunta, sun ƙẽwaye da su.
-
وَإِن يَسْتَغِيثُوا يُغَاثُوا بِمَاءٍ كَالْمُهْلِ يَشْوِي الْوُجُوهَ ۚ بِئْسَ الشَّرَابُ وَسَاءَتْ مُرْتَفَقًا ٢٩
Wa in yastaghisu yughasu bi ma'in kal muhli yashwil wujuha bi'sash sharabu wa sa'at murtafaqa
Kuma idan sun nẽmi taimako sai a taimake su da wani ruwa kamar dabzar mai, yanã sõye fuskõki. Tir da abin shansu, kuma wutar ta yi mũnin zama mahũtarsu.
-
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجْرَ مَنْ أَحْسَنَ عَمَلًا ٣٠
Innal lazina amanu wa 'amilus salihati inna la nudi'u ajra man ahsana 'amala
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai lalle ne Mũ bã Mu tõzartar da lãdar wanda ya kyautata aiki.
-
أُولَٰئِكَ لَهُمْ جَنَّاتُ عَدْنٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهِمُ الْأَنْهَارُ يُحَلَّوْنَ فِيهَا مِنْ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٍ وَيَلْبَسُونَ ثِيَابًا خُضْرًا مِّن سُندُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُّتَّكِئِينَ فِيهَا عَلَى الْأَرَائِكِ ۚ
Ula'ika lahum jannatu 'adnin tajri min tahtihimul anharu yuhallauna fiha min asawira min zahabin wa yalbasuna siyaban khudram min sundusin wa istabraqim muttaki'ina fiha 'alal ara'ik
Waɗannan sunã da gidãjen Aljannar zama, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, anã sanya musu ƙawa, a cikinsu, daga mundãye na zinariya, kuma sunã tufantar waɗansu tũfãfi kõre, na alharĩni raƙĩƙi da alharini mai kauri sunã kishingiɗe a cikinsu, a kan, karagu.
-
نِعْمَ الثَّوَابُ وَحَسُنَتْ مُرْتَفَقًا ٣١
Ni'mas sawabu wa hasunat murtafaqa
Mãdalla da sakamakonsu. Kuma Aljanna ta kyautatu da zama wurin hutãwa.
-
وَاضْرِبْ لَهُم مَّثَلًا رَّجُلَيْنِ جَعَلْنَا لِأَحَدِهِمَا جَنَّتَيْنِ مِنْ أَعْنَابٍ وَحَفَفْنَاهُمَا بِنَخْلٍ وَجَعَلْنَا بَيْنَهُمَا زَرْعًا ٣٢
Wadrib lahum masalar rajulaini ja'alna li ahadihima jannataini min a'nabin wa hafafnahuma bi nakhlin wa ja'alna bainahuma zar'a
Kuma ka buga musu misãli da waɗansu maza biyu. Mun sanya wa ɗayansu gõnaki biyu na inabõbi, kuma Muka kẽwayesu da itãcen dabĩnai, kuma Muka sanya shũka a tsakãninsu (sũ gõnakin).
-
كِلْتَا الْجَنَّتَيْنِ آتَتْ أُكُلَهَا وَلَمْ تَظْلِم مِّنْهُ شَيْئًا ۚ وَفَجَّرْنَا خِلَالَهُمَا نَهَرًا ٣٣
Kiltal jannataini atat ukulaha wa lam tazlim minhu shai'an wa fajjarna khilalahuma nahara
Kõwace gõna daga biyun, tã bãyar da amfãninta, kuma ba ta yi zãluncin kõme ba daga gare shi. Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙoramu a tsakãninsu.
-
وَكَانَ لَهُ ثَمَرٌ فَقَالَ لِصَاحِبِهِ وَهُوَ يُحَاوِرُهُ أَنَا أَكْثَرُ مِنكَ مَالًا وَأَعَزُّ نَفَرًا ٣٤
Wa kana lahu samarun fa qala li sahibihi wa huwa yuhawiruhu ana aksaru minka malan wa a'azzu nafara
Kuma ɗan ĩtãce ya kasance gare shi. Sai ya ce wa abõkinsa, alhali kuwa yanã muhãwara da shi, "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare ka a wajen dũkiya, kuma mafi izza a wajen jama'a."
-
وَدَخَلَ جَنَّتَهُ وَهُوَ ظَالِمٌ لِّنَفْسِهِ قَالَ مَا أَظُنُّ أَن تَبِيدَ هَٰذِهِ أَبَدًا ٣٥
Wa dakhala jannatahu wa huwa zalimul li nafsihi qala ma azunnu an tabida hazihi abada
Kuma ya shiga gõnarsa, alhãli yanã mai zãlunci ga kansa, ya ce: "Bã ni zaton wannan zã ta halaka har abada."
-
وَمَا أَظُنُّ السَّاعَةَ قَائِمَةً وَلَئِن رُّدِدتُّ إِلَىٰ رَبِّي لَأَجِدَنَّ خَيْرًا مِّنْهَا مُنقَلَبًا ٣٦
Wa ma azunnus sa'ata qa'imatan wa la'ir rudittu ila rabbi la ajidanna khairam minha munqalaba
"Kuma bã ni zaton sa'a mai tsayuwa ce, kuma lalle ne, idan an mayar da ni zuwa ga Ubangijiĩna, to, lalle ne, zan sãmi abin da yake mafi alhẽri daga gare ta ya zama makõma."
-
قَالَ لَهُ صَاحِبُهُ وَهُوَ يُحَاوِرُهُ أَكَفَرْتَ بِالَّذِي خَلَقَكَ مِن تُرَابٍ ثُمَّ مِن نُّطْفَةٍ ثُمَّ سَوَّاكَ رَجُلًا ٣٧
Qala lahu sahibuhu wa huwa yuhawiruhu akafarta bil lazi khalaqaka min turabin summa min nutfatin summa sawwaka rajula
Abõkinsa ya ce masa, alhãli kuwa yanã muhãwara da shi, "Ashe kã kãfirta da wanda Ya halitta ka daga turɓaya, sa'an nan daga ɗigon maniyi, sa, an nan Ya daidaita ka, ka zama mutum?"
-
لَّٰكِنَّا هُوَ اللَّهُ رَبِّي وَلَا أُشْرِكُ بِرَبِّي أَحَدًا ٣٨
Lakinna huwallahu rabbi wa la ushriku bi rabbi ahada
"Amma ni, shĩ ne Allah Ubangijina, kuma bã zan tãra kõwa da Ubangijina ba"
-
وَلَوْلَا إِذْ دَخَلْتَ جَنَّتَكَ قُلْتَ مَا شَاءَ اللَّهُ لَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ ۚ إِن تَرَنِ أَنَا أَقَلَّ مِنكَ مَالًا وَوَلَدًا ٣٩
Wa laula iz dakhalta jannataka qulta ma sha'allahu la quwwata illa billahi in tarani ana aqalla minka malan wa walada
"Kuma don me, a lõkacin da ka shiga gõnarka, ka, ce, 'Abin da Allah ya so (shi ke tabbata) bãbu wani ƙarfi fãce game da Allah.' Idan ka gan ni, ni ne mafi ƙaranci daga gare ka a wajen dũkiya da ɗiya."
-
فَعَسَىٰ رَبِّي أَن يُؤْتِيَنِ خَيْرًا مِّن جَنَّتِكَ وَيُرْسِلَ عَلَيْهَا حُسْبَانًا مِّنَ السَّمَاءِ فَتُصْبِحَ صَعِيدًا زَلَقًا ٤٠
Fa 'asa rabbi an yu'tiyani khairam min jannatika wa yursila 'alaiha husbanam minas sama'i fa tusbiha sa'idan zalaqa
"To, akwai fãtan Ubangijĩna Ya ba ni abin da yake mafi alhẽri daga gõnarka, kuma ya aika azãba a kanta (ita gõnarka) daga sama, sai ta wãyi gari turɓãya mai santsi."
-
أَوْ يُصْبِحَ مَاؤُهَا غَوْرًا فَلَن تَسْتَطِيعَ لَهُ طَلَبًا ٤١
Aw yusbiha ma'uha ghauran fa lan tastati'a lahu talaba
"Kõ kuma ruwanta ya wãyi gari faƙaƙƙe, sabõda haka, bã zã ka iya nẽmo shi ba dõminta."
-
وَأُحِيطَ بِثَمَرِهِ فَأَصْبَحَ يُقَلِّبُ كَفَّيْهِ عَلَىٰ مَا أَنفَقَ فِيهَا وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا وَيَقُولُ يَا لَيْتَنِي لَمْ أُشْرِكْ بِرَبِّي أَحَدًا ٤٢
Wa uhita bi samarihi fa asbaha yuqallibu kaffaihi 'ala ma anfaqa fiha wa hiya khawiyatun 'ala 'urushiha wa yaqulu ya laitani lam ushrik bi rabbi ahada
Kuma aka halaka dukan 'ya'yan itãcensa, sai ya wãyi gari yanã jũyar da tãfunansa biyu, sabõda abin da ya kashe a cikinta, alhãli kuwa ita tanã kwance a kan rassanta, kuma yanã cẽwa, "Kaitõna, dã dai ban tãra wani da Ubangijina ba!"
-
وَلَمْ تَكُن لَّهُ فِئَةٌ يَنصُرُونَهُ مِن دُونِ اللَّهِ وَمَا كَانَ مُنتَصِرًا ٤٣
Wa lam takul lahu fi'atun yansurunahu min dunillahi wa ma kana muntasira
Kuma wata jama'a ba ta kasance a gare shi ba, waɗanda ke taimakon sa, baicin Allah, kuma bai kasance mai taimakon kansa ba.
-
هُنَالِكَ الْوَلَايَةُ لِلَّهِ الْحَقِّ ۚ هُوَ خَيْرٌ ثَوَابًا وَخَيْرٌ عُقْبًا ٤٤
Hunalikal walayatu lillahil haqqi huwa khairun sawaban wa khairun 'uqba
A can taimako da jiɓinta ga Allah yake. Shĩ ne kawai Gaskiya, shĩ ne Mafĩfĩci ga lãda kuma Mafĩ fĩci ga ãƙiba.
-
وَاضْرِبْ لَهُم مَّثَلَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا كَمَاءٍ أَنزَلْنَاهُ مِنَ السَّمَاءِ فَاخْتَلَطَ بِهِ نَبَاتُ الْأَرْضِ فَأَصْبَحَ هَشِيمًا تَذْرُوهُ الرِّيَاحُ ۗ
Wadrib lahum masalal hayatid dunya ka ma'in anzalnahu minas sama'i fakhtalata bihi nabatul ardi fa asbaha hashiman tazruhur riyah
Ka buga musu misãlin rãyuwar dũniya, kamar ruwane wanda Muka saukar da shi daga sama sa'an nan tsirin ƙasa ya garwaya da shi, sa'an nan ya wãyi gari dudduga, iska tanã shiƙar sa.
-
وَكَانَ اللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ مُّقْتَدِرًا ٤٥
Wa kanallahu 'ala kulli shai'im muqtadira
Kuma Allah Ya kasance Mai yawan ĩkon yi ne a kan dukan kõme.
-
الْمَالُ وَالْبَنُونَ زِينَةُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۖ وَالْبَاقِيَاتُ الصَّالِحَاتُ خَيْرٌ عِندَ رَبِّكَ ثَوَابًا وَخَيْرٌ أَمَلًا ٤٦
Al malu wal banuna zinatul hayatid dunya wal baqiyatus salihatu khairun 'inda rabbika sawaban wa khairun amala
Dũkiya da ɗiya, sũ ne ƙawar rãyuwar dũniya, kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai sun fi zama alhẽri a wurin Ubangijinka ga lãda kuma sun fi alhẽri ga bũri.
-
وَيَوْمَ نُسَيِّرُ الْجِبَالَ وَتَرَى الْأَرْضَ بَارِزَةً وَحَشَرْنَاهُمْ فَلَمْ نُغَادِرْ مِنْهُمْ أَحَدًا ٤٧
Wa yauma nusayyirul jibala wa taral arda barizatan wa hasharnahum fa lam nughadir minhum ahada
Kuma a rãnar da Muke tafiyar da duwãtsu, kuma ka ga ƙasa bayyane, kuma Mu tãra su har ba Mu bar kõwa ba daga gare su.
-
وَعُرِضُوا عَلَىٰ رَبِّكَ صَفًّا لَّقَدْ جِئْتُمُونَا كَمَا خَلَقْنَاكُمْ أَوَّلَ مَرَّةٍ ۚ بَلْ زَعَمْتُمْ أَلَّن نَّجْعَلَ لَكُم مَّوْعِدًا ٤٨
Wa 'uridu 'ala rabbika saffal laqad ji'tumuna kama khalaqnakum awwala marratin bal za'amtum allan naj'ala lakum mau'ida
Kuma a gittã su ga Ubangijinka sunã sahu guda, (Mu ce musu), "Lalle ne haƙĩƙa kun zo Mana, kamar yadda Muka halitta ku a farkon lõkaci. Ã'a, kun riya cẽwa bã zã Mu sanya mukuwani lõkacin haɗuwa ba."
-
وَوُضِعَ الْكِتَابُ فَتَرَى الْمُجْرِمِينَ مُشْفِقِينَ مِمَّا فِيهِ وَيَقُولُونَ يَا وَيْلَتَنَا مَالِ هَٰذَا الْكِتَابِ لَا يُغَادِرُ صَغِيرَةً وَلَا كَبِيرَةً إِلَّا أَحْصَاهَا ۚ
Wa wudi'al kitabu fa taral mujrimina mushfiqina mimma fihi wa yaquluna ya wailatana mali hazal kitabi la yughadiru saghiratan wa la kabiratan illa ahsaha
Kuma aka aza littãfin ayyuka, sai ka ga mãsu laifi sunã mãsu jin tsõro daga abin da ke cikinsa, kuma sunã cẽwa "Kaitonmu! Mẽne ne ga wannan littãfi, bã ya barin ƙarama, kuma bã ya barin babba, fãce yã ƙididdige ta?"
-
وَوَجَدُوا مَا عَمِلُوا حَاضِرًا ۗ وَلَا يَظْلِمُ رَبُّكَ أَحَدًا ٤٩
Wa wajadu ma 'amilu hadiran wa la yazlimu rabbuka ahada
Kuma suka sãmi abin da suka aikata halarce. Kuma Ubangijinka bã Ya zãluntar kõwa.
-
وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلَائِكَةِ اسْجُدُوا لِآدَمَ فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ كَانَ مِنَ الْجِنِّ فَفَسَقَ عَنْ أَمْرِ رَبِّهِ ۗ
Wa iz qulna lil mala'ikatisjudu li Adama fa sajadu illa Iblisa kana minal jinni fa fasaqa 'an amri rabbih
Kuma a lõkacin da Muka ce wa malãiku, "Ku yi sujada ga Ãdamu." Sai suka yi sujada fãce Iblĩsa, yã kasance daga aljannu sai ya yi fãsiƙanci ga barin umurnin Ubangijinsa,
-
أَفَتَتَّخِذُونَهُ وَذُرِّيَّتَهُ أَوْلِيَاءَ مِن دُونِي وَهُمْ لَكُمْ عَدُوٌّ ۚ بِئْسَ لِلظَّالِمِينَ بَدَلًا ٥٠
Afatattakhizunahu wa zurriyyatahu auliya'a min duni wa hum lakum 'aduwwun bi'sa liz zalimina badala
To fa, ashe, kunã riƙon sa, shi da zũriyarsa, su zama majiɓinta baicin Ni, alhãli kuwa su maƙiya ne a gare ku? Tir da ya zama musanya ga azzãlumai.
-
مَّا أَشْهَدتُّهُمْ خَلْقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَلَا خَلْقَ أَنفُسِهِمْ وَمَا كُنتُ مُتَّخِذَ الْمُضِلِّينَ عَضُدًا ٥١
Ma ashhattuhum khalqas samawati wal ardi wa la khalqa anfusihim wa ma kuntu muttakhizal mudillina 'aduda
Ban shaida musu halittar sammai da ƙasa ba, kuma ban (shaida musu) halittar rãyukansu ba kuma ban kasance mai riƙon mãsu ɓatarwa (da wani) su zama mataimaka ba.
-
وَيَوْمَ يَقُولُ نَادُوا شُرَكَائِيَ الَّذِينَ زَعَمْتُمْ فَدَعَوْهُمْ فَلَمْ يَسْتَجِيبُوا لَهُمْ وَجَعَلْنَا بَيْنَهُم مَّوْبِقًا ٥٢
Wa yauma yaqulu nadu shuraka'iyal lazina za'amtum fa da'auhum fa lam yastajibu lahum wa ja'alna bainahum maubiqa
Kuma da rãnar da Allah Yake cẽwa, "Ku kirãyi abõkan tarayyãTa, waɗanda kuka riya." Sai su kirãye su, sai bã zã su karɓa musu ba, kuma Mu sanya Maubiƙa (Mahalaka) a tsakãninsu,
-
وَرَأَى الْمُجْرِمُونَ النَّارَ فَظَنُّوا أَنَّهُم مُّوَاقِعُوهَا وَلَمْ يَجِدُوا عَنْهَا مَصْرِفًا ٥٣
Wa ra'al mujrimunan nara fa zannu annahum muwaqi'uha wa lam yajidu 'anha masrifa
Kuma mãsu laifi suka ga wutã suka tabbata lalle ne, sũ mãsu, auka mata ne, kuma ba su sãmi majũya ba daga gare ta.
-
وَلَقَدْ صَرَّفْنَا فِي هَٰذَا الْقُرْآنِ لِلنَّاسِ مِن كُلِّ مَثَلٍ ۚ وَكَانَ الْإِنسَانُ أَكْثَرَ شَيْءٍ جَدَلًا ٥٤
Wa laqad sarrafna fi hazal qur'ani lin nasi min kulli masalin wa kanal insanu aksara shai'in jadala
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun jujjũya, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane irin misãli ga mutãne (dõmin su gãne, su bi sharĩ'a), kuma mutum yã kasance mafi yawan abu ga jidãli.
-
وَمَا مَنَعَ النَّاسَ أَن يُؤْمِنُوا إِذْ جَاءَهُمُ الْهُدَىٰ وَيَسْتَغْفِرُوا رَبَّهُمْ إِلَّا أَن تَأْتِيَهُمْ سُنَّةُ الْأَوَّلِينَ أَوْ يَأْتِيَهُمُ الْعَذَابُ قُبُلًا ٥٥
Wa ma mana'an nasa an yu'minu iz ja'ahumul huda wa yastaghfiru rabbahum illa an ta'tiyahum sunnatul awwalina au ya'tiyahumul 'azabu qubula
Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni a lõkacinda shiriya ta zo musu, kuma su nẽmi gãfara daga Ubangijinsu, fãce hanyar farko ta je musu kõ kuma azãba ta jẽ musu nau'i-nau'i.
-
وَمَا نُرْسِلُ الْمُرْسَلِينَ إِلَّا مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ ۚ وَيُجَادِلُ الَّذِينَ كَفَرُوا بِالْبَاطِلِ لِيُدْحِضُوا بِهِ الْحَقَّ ۖ وَاتَّخَذُوا آيَاتِي وَمَا أُنذِرُوا هُزُوًا ٥٦
Wa ma nursilul mursalina illa mubashshirina wa munzirina wa yujadilul lazina kafaru bil batili li yudhidu bihil haqqa wattakhazu ayati wa ma unziru huzuwa
Kuma ba Mu aika Manzanni ba fãce sunã mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi, kuma waɗanda suka kãfirta sunã jidãli da ƙarya dõmin su ɓãta gaskiya da ita, kuma suka riƙi ãyõyi Na da abin da aka yi musu gargaɗi da shi abin izgili.
-
وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّن ذُكِّرَ بِآيَاتِ رَبِّهِ فَأَعْرَضَ عَنْهَا وَنَسِيَ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ ۚ
Wa man azlamu mimman zukkira bi ayati rabbihi fa a'rada 'anha wa nasiya ma qaddamat yadah
Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda aka tunãtar game da ãyõyin Ubangijinsa, sai ya bijire daga barinsu, kuma ya manta abin da hannãyensa suka gabãtar?
-
إِنَّا جَعَلْنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ أَكِنَّةً أَن يَفْقَهُوهُ وَفِي آذَانِهِمْ وَقْرًا ۖ
Inna ja'alna 'ala qulubihim akinnatan an yafqahuhu wa fi azanihim waqra
Lalle ne Mũ, Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi, kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi,
-
وَإِن تَدْعُهُمْ إِلَى الْهُدَىٰ فَلَن يَهْتَدُوا إِذًا أَبَدًا ٥٧
Wa in tad'uhum ilal huda fa lan yahtadu izan abada
kuma idan kã kĩrayẽ su zuwa ga shiriya, to, bã zã su shiryu ba, a sa'an nan, har abada.
-
وَرَبُّكَ الْغَفُورُ ذُو الرَّحْمَةِ ۖ لَوْ يُؤَاخِذُهُم بِمَا كَسَبُوا لَعَجَّلَ لَهُمُ الْعَذَابَ ۚ بَل لَّهُم مَّوْعِدٌ لَّن يَجِدُوا مِن دُونِهِ مَوْئِلًا ٥٨
Wa rabbukal ghafuru zur rahmati lau yu'akhizuhum bima kasabu la 'ajjala lahumul 'azaba bal lahum mau'idul lan yajidu min dunihi mau'ila
Kuma Ubangijinka Mai gãfara ne, Ma'abũcin rahama. Dã Yanã kãma su sabõda abin da suka sanã'anta, lalle ne, dã Ya gaggauta azãba a gare su. Ã'a, sunã da lõkacin alkawari, (wanda) bã zã su sãmi wata makõma ba, baicinSa.
-
وَتِلْكَ الْقُرَىٰ أَهْلَكْنَاهُمْ لَمَّا ظَلَمُوا وَجَعَلْنَا لِمَهْلِكِهِم مَّوْعِدًا ٥٩
Wa tilkal qura ahlaknahum lamma zalamu wa ja'alna li mahlikihim mau'ida
Kuma waɗancan alƙaryu Mun halaka su, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma Muka sanya lõkacin alkawarin, ga halaka su.
-
وَإِذْ قَالَ مُوسَىٰ لِفَتَاهُ لَا أَبْرَحُ حَتَّىٰ أَبْلُغَ مَجْمَعَ الْبَحْرَيْنِ أَوْ أَمْضِيَ حُقُبًا ٦٠
Wa iz qala Musa li fatahu la abrahu hatta ablugha majma'al bahraini au amdiya huquba
Kuma a lõkacin da Mũsã ya ce wa yãronsa, "Bã zan gushe ba sai na isa mahaɗar tẽku biyu, kõ in shũɗe da tafiya shekara da shẽkaru."
-
فَلَمَّا بَلَغَا مَجْمَعَ بَيْنِهِمَا نَسِيَا حُوتَهُمَا فَاتَّخَذَ سَبِيلَهُ فِي الْبَحْرِ سَرَبًا ٦١
Fa lamma balagha majma'a bainihima nasiya hutahuma fattakhaza sabilahu fil bahri saraba
To, a lõkacin da suka isa mahaɗar tsakãninsu sai suka manta kĩfinsu, sai ya kãma tafarkinsa a cikin tẽku kamar bĩga.
-
فَلَمَّا جَاوَزَا قَالَ لِفَتَاهُ آتِنَا غَدَاءَنَا لَقَدْ لَقِينَا مِن سَفَرِنَا هَٰذَا نَصَبًا ٦٢
Fa lamma jawaza qala li fatahu atina ghada'ana laqad laqina min safarina haza nasaba
To, a lõkacin da suka wuce ya ce wa yãronsa, "Ka kãwo mana kãlãcinmu. Lalle ne haƙĩƙa mun haɗu da wahala daga tafiyarmu wannan."
-
قَالَ أَرَأَيْتَ إِذْ أَوَيْنَا إِلَى الصَّخْرَةِ فَإِنِّي نَسِيتُ الْحُوتَ وَمَا أَنسَانِيهُ إِلَّا الشَّيْطَانُ أَنْ أَذْكُرَهُ ۚ
Qala ara'aita iz awaina ilas sakhrati fa inni nasitul huta wa ma ansanihu illash shaitanu an azkurah
(Yãron) ya ce: "Kã gani! A lõkacin da muka tattara zuwa ga falalen nan to, lalle nĩ, na manta kĩfin, kuma bãbu abin da yamantar da nĩ shi, fãce Shaiɗan, dõmin kada in tuna shi,
-
وَاتَّخَذَ سَبِيلَهُ فِي الْبَحْرِ عَجَبًا ٦٣
Wattakhaza sabilahu fil bahri 'ajaba
sai ya kama tafarkinsa a cikin tẽku, da mãmãki!"
-
قَالَ ذَٰلِكَ مَا كُنَّا نَبْغِ ۚ فَارْتَدَّا عَلَىٰ آثَارِهِمَا قَصَصًا ٦٤
Qala zalika ma kunna nabghi fartadda 'ala asarihima qasasa
Ya ce: "Wancan ne abin da muka kasance munã biɗã." Sai suka kõma a kan gurãbunsu, sunã bĩbiya.
-
فَوَجَدَا عَبْدًا مِّنْ عِبَادِنَا آتَيْنَاهُ رَحْمَةً مِّنْ عِندِنَا وَعَلَّمْنَاهُ مِن لَّدُنَّا عِلْمًا ٦٥
Fa wajada 'abdam min 'ibadina atainahu rahmatam min 'indina wa 'allamnahu mil ladunna 'ilma
Sai suka sãmi wani bãwa daga bãyin Mu, Mun bã shi wata rahama daga wurin Mu, kuma Mun sanar da shi wani ilmi daga gun Mu.
-
قَالَ لَهُ مُوسَىٰ هَلْ أَتَّبِعُكَ عَلَىٰ أَن تُعَلِّمَنِ مِمَّا عُلِّمْتَ رُشْدًا ٦٦
Qala lahu Musa hal attabi'uka 'ala an tu'allimani mimma 'ullimta rushda
Mũsã ya ce masa, "Ko in bĩ ka a kan ka sanar da ni daga abin da aka sanar da kai na shiriya?"
-
قَالَ إِنَّكَ لَن تَسْتَطِيعَ مَعِيَ صَبْرًا ٦٧
Qala innaka lan tastati'a ma'iya sabra
Ya ce: "Lalle ne kai bã zã ka iya yin haƙuri tãre da nĩ, ba."
-
وَكَيْفَ تَصْبِرُ عَلَىٰ مَا لَمْ تُحِطْ بِهِ خُبْرًا ٦٨
Wa kaifa tasbiru 'ala ma lam tuhit bihi khubra
"Kuma yãya zã ka yi haƙuri a kan abin da ba ka kẽwayeda shi ba ga jarrabãwa?"
-
قَالَ سَتَجِدُنِي إِن شَاءَ اللَّهُ صَابِرًا وَلَا أَعْصِي لَكَ أَمْرًا ٦٩
Qala sa tajiduni in sha'allahu sabiran wa la a'si laka amra
Ya ce: "Za ka sãme ni, in Allah Yã so mai haƙuri kuma bã zan sãɓa maka ba ga wani umurni."
-
قَالَ فَإِنِ اتَّبَعْتَنِي فَلَا تَسْأَلْنِي عَن شَيْءٍ حَتَّىٰ أُحْدِثَ لَكَ مِنْهُ ذِكْرًا ٧٠
Qala fa inittaba'tani fa la tas'alni 'an shai'in hatta uhdisa laka minhu zikra
Ya ce: "To idan ka bĩ ni to kada ka tambaye ni daga kõme sai na lãbarta maka ambato daga gare shi."
-
فَانطَلَقَا حَتَّىٰ إِذَا رَكِبَا فِي السَّفِينَةِ خَرَقَهَا ۖ قَالَ أَخَرَقْتَهَا لِتُغْرِقَ أَهْلَهَا لَقَدْ جِئْتَ شَيْئًا إِمْرًا ٧١
Fantalaqa hatta iza rakiba fis safinati kharaqaha qala akharaqtaha li tughriqa ahlaha laqad ji'ta shai'an imra
Sai suka tafi har a lõkacin da suka hau a cikin jirgi, ya hũje shi, ya ce, "Kã hũje shi dõmin ya nutsar da mutãnensa? Lalle ne, haƙĩƙa, kã zo da wani babban abu!"
-
قَالَ أَلَمْ أَقُلْ إِنَّكَ لَن تَسْتَطِيعَ مَعِيَ صَبْرًا ٧٢
Qala alam aqul innaka lan tastati'a ma'iya sabra
Ya ce: "Ashe ban ce, lalle kai, bã za ka iya yin haƙuri tãre da ni ba?"
-
قَالَ لَا تُؤَاخِذْنِي بِمَا نَسِيتُ وَلَا تُرْهِقْنِي مِنْ أَمْرِي عُسْرًا ٧٣
Qala la tu'akhizni bima nasitu wa la turhiqni min amri 'usra
Ya ce: "Kada ka kãma ni da abin da na manta kuma kada ka kallafa mini tsanani ga al'amarĩna."
-
فَانطَلَقَا حَتَّىٰ إِذَا لَقِيَا غُلَامًا فَقَتَلَهُ قَالَ أَقَتَلْتَ نَفْسًا زَكِيَّةً بِغَيْرِ نَفْسٍ لَّقَدْ جِئْتَ شَيْئًا نُّكْرًا ٧٤
Fantalaqa hatta iza laqiya ghulaman fa qatalahu qala aqatalta nafsan zakiyyatan bi ghairi nafsil laqad ji'ta shai'an nukra
Sai suka tafi, har suka haɗu da wani yãro, sai ya kashe shi. Ya ce: "Ashe kã kashe rai tsarkakakke, bã da wani rai ba? Lalle ne haƙĩƙa ka zo da wani abu na ƙyãma."
-
قَالَ أَلَمْ أَقُل لَّكَ إِنَّكَ لَن تَسْتَطِيعَ مَعِيَ صَبْرًا ٧٥
Qala alam aqul laka innaka lan tastati'a ma'iya sabra
Ya ce: "Shin, ban ce maka ba, lalle ne kai bã zã ka iya yin haƙuri tãre da nĩ ba?"
-
قَالَ إِن سَأَلْتُكَ عَن شَيْءٍ بَعْدَهَا فَلَا تُصَاحِبْنِي ۖ قَدْ بَلَغْتَ مِن لَّدُنِّي عُذْرًا ٧٦
Qala in sa'altuka 'an shai'in ba'daha fa la tusahibni qad balaghta mil ladunni 'uzra
Ya ce: "Idan na tambaye ka daga wani abu a bãyanta, to, kada ka abũce ni. Lalle ne, kã isa ga iyakar uzuri daga gare ni."
-
فَانطَلَقَا حَتَّىٰ إِذَا أَتَيَا أَهْلَ قَرْيَةٍ اسْتَطْعَمَا أَهْلَهَا فَأَبَوْا أَن يُضَيِّفُوهُمَا فَوَجَدَا فِيهَا جِدَارًا يُرِيدُ أَن يَنقَضَّ فَأَقَامَهُ ۖ
Fantalaqa hatta iza ataya ahla qaryatinistat'ama ahlaha fa abau an yudayyifuhuma fa wajada fiha jidaran yuridu an yanqadda fa aqamah
Sai suka tafi, har a lõkacin da suka je wa mutãnen wata alƙarya, suka nẽmi mutãnenta da su bã su abinci, sai suka ƙi su yi musu liyãfa. Sai suka sãmi wani bango a cikinta yanã nufin ya karye, sai (Halliru) ya tãyar da shi mĩƙe.
-
قَالَ لَوْ شِئْتَ لَاتَّخَذْتَ عَلَيْهِ أَجْرًا ٧٧
Qala lau shi'ta lattakhazta 'alaihi ajra
(Mũsã) ya ce: "Dã kã so, lalle ne dã kã karɓi ijãra a kansa."
-
قَالَ هَٰذَا فِرَاقُ بَيْنِي وَبَيْنِكَ ۚ سَأُنَبِّئُكَ بِتَأْوِيلِ مَا لَمْ تَسْتَطِع عَّلَيْهِ صَبْرًا ٧٨
Qala haza firaqu baini wa bainika sa unabbi'uka bi ta'wili ma lam tastati' 'alaihi sabra
Ya ce: "Wannan shi ne rabuwar tsakanina da tsakaninka. Zã ni gaya maka fassarar abin da ba ka iya yin haƙuri ba a kansa."
-
أَمَّا السَّفِينَةُ فَكَانَتْ لِمَسَاكِينَ يَعْمَلُونَ فِي الْبَحْرِ فَأَرَدتُّ أَنْ أَعِيبَهَا وَكَانَ وَرَاءَهُم مَّلِكٌ يَأْخُذُ كُلَّ سَفِينَةٍ غَصْبًا ٧٩
Ammas safinatu fa kanat li masakina ya'maluna fil bahri fa arattu an a'ibaha wa kana wara'ahum malikun ya'khuzu kulla safinatin ghasba
"Amma Jirgin, to, ya zama na waɗansu matalauta ne sunã aiki a cikin tẽku, sai na yi niyyar in aibanta shi, alhãli kuwa wani sarki ya kasance a gaba gare su, yanã karɓẽwar kõwane jirgi (lãfiyayye) da ƙwãce.
-
وَأَمَّا الْغُلَامُ فَكَانَ أَبَوَاهُ مُؤْمِنَيْنِ فَخَشِينَا أَن يُرْهِقَهُمَا طُغْيَانًا وَكُفْرًا ٨٠
Wa ammal ghulamu fa kana abawahu mu'minaini fa khashina an yurhiqahuma tughyanan wa kufra
"Kuma amma yaron, to, uwãyensa sun kasance mũminai, to, sai muka ji tsõron ya kallafa musu kangara da kãfirci."
-
فَأَرَدْنَا أَن يُبْدِلَهُمَا رَبُّهُمَا خَيْرًا مِّنْهُ زَكَاةً وَأَقْرَبَ رُحْمًا ٨١
Fa aradna an yubdilahuma rabbuhuma khairam minhu zakatan wa aqraba ruhma
"Sai muka yi nufin Ubangijinsu Ya musanya musu mafi alhẽri daga gare shi ga tsarkakuwa, kuma mafi kusantar tausayi."
-
وَأَمَّا الْجِدَارُ فَكَانَ لِغُلَامَيْنِ يَتِيمَيْنِ فِي الْمَدِينَةِ وَكَانَ تَحْتَهُ كَنزٌ لَّهُمَا وَكَانَ أَبُوهُمَا صَالِحًا فَأَرَادَ رَبُّكَ أَن يَبْلُغَا أَشُدَّهُمَا وَيَسْتَخْرِجَا كَنزَهُمَا رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ ۚ
Wa ammal jidaru fa kana li ghulamaini yatimaini fil madinati wa kana tahtahu kanzul lahuma wa kana abuhuma salihan fa arada rabbuka an yablugha ashuddahuma wa yastakhrija kanzahuma rahmatam mir rabbik
"Kuma amma bangon, to, yã kasance na waɗansu yãra biyu ne, marãyu a cikin birnin, kuma akwai wata taska tãsu a ƙarƙashinsa, kuma ubansu ya kasance sahĩhin mutum ne, dõmin haka Ubangijinka Ya yi nufin su isa iyãkar ƙarfinsu, kuma sũ, su fitar da taskarsu, sabõda rahama ne daga Ubangijinka.
-
وَمَا فَعَلْتُهُ عَنْ أَمْرِي ۚ ذَٰلِكَ تَأْوِيلُ مَا لَمْ تَسْطِع عَّلَيْهِ صَبْرًا ٨٢
Wa ma fa'altuhu 'an amri zalika ta'wilu ma lam tasti' 'alaihi sabra
Kuma ban yi shi ba daga umurnĩna. Wancan shĩ ne fassarar abin da ba ka iya yin haƙuri ba a kansa."
-
وَيَسْأَلُونَكَ عَن ذِي الْقَرْنَيْنِ ۖ قُلْ سَأَتْلُو عَلَيْكُم مِّنْهُ ذِكْرًا ٨٣
Wa yas'alunaka 'an zil Qarnaini qul sa atlu 'alaikum minhu zikra
Kuma suna tambayar ka daga zulƙarnaini, ka ce: "Zan karanta muku ambato daga gare shi."
-
إِنَّا مَكَّنَّا لَهُ فِي الْأَرْضِ وَآتَيْنَاهُ مِن كُلِّ شَيْءٍ سَبَبًا ٨٤
Inna makkanna lahu fil ardi wa atainahu min kulli shai'in sababa
Lalle ne Mũ Mun bã shi mulki a cikin ƙasa kuma Muka bã shi daga kõwane abu, hanya (zuwa ga murãdinsa).
-
فَأَتْبَعَ سَبَبًا ٨٥
Fa atba'a sababa
Sai ya bi hanya.
-
حَتَّىٰ إِذَا بَلَغَ مَغْرِبَ الشَّمْسِ وَجَدَهَا تَغْرُبُ فِي عَيْنٍ حَمِئَةٍ وَوَجَدَ عِندَهَا قَوْمًا ۗ
Hatta iza balagha maghribash shamsi wajadaha taghrubu fi 'ainin hami'atin wa wajada 'indaha qauma
Har a lõkacin da ya isa ga mafãɗar rãnã, kuma ya sãme ta tanã ɓacẽwa a cikin wani ruwa mai baƙar lãkã, kuma ya sãmi waɗansu mutãne a wurinta.
-
قُلْنَا يَا ذَا الْقَرْنَيْنِ إِمَّا أَن تُعَذِّبَ وَإِمَّا أَن تَتَّخِذَ فِيهِمْ حُسْنًا ٨٦
Qulna ya zal Qarnaini imma an tu'azziba wa imma an tattakhiza fihim husna
Muka ce: "Yã Zulƙarnaini imma dai ka azabtar kuma imma ka riƙi kyautatãwa a cikinsu."
-
قَالَ أَمَّا مَن ظَلَمَ فَسَوْفَ نُعَذِّبُهُ ثُمَّ يُرَدُّ إِلَىٰ رَبِّهِ فَيُعَذِّبُهُ عَذَابًا نُّكْرًا ٨٧
Qala amma man zalama fa saufa nu'azzibuhu summa yuraddu ila rabbihi fa yu'azzibuhu 'azaban nukra
Ya ce: "Amma wanda ya yi zãlunci, to zã mu azabta shi, sa'an nan a mayar da shi zuwa ga Ubangijinsa, sai kuma Ya yi masa azãba, azãba abar ƙyãma."
-
وَأَمَّا مَنْ آمَنَ وَعَمِلَ صَالِحًا فَلَهُ جَزَاءً الْحُسْنَىٰ ۖ وَسَنَقُولُ لَهُ مِنْ أَمْرِنَا يُسْرًا ٨٨
Wa amma man amana wa 'amila salihan fa lahu jaza'anil husna wa sa naqulu lahu min amrina yusra
"Kuma amma wanda ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin ƙwarai to, zã mu yi sakamako a gare shi (watau kyauta) mai kyau, kuma zã mu gaya masa sauƙi daga umurninmu."
-
ثُمَّ أَتْبَعَ سَبَبًا ٨٩
Summa atba'a sababa
Sa'an nan kuma ya bi hanya.
-
حَتَّىٰ إِذَا بَلَغَ مَطْلِعَ الشَّمْسِ وَجَدَهَا تَطْلُعُ عَلَىٰ قَوْمٍ لَّمْ نَجْعَل لَّهُم مِّن دُونِهَا سِتْرًا ٩٠
Hatta iza balagha matli'ash shamsi wajadaha tatlu'u 'ala qaumil lam naj'al lahum min duniha sitra
Har a lõkacin da ya isa ga mafitar rãnã, ya sãme ta tanã fita a kan waɗansu mutãne (waɗanda) ba Mu sanya musu wata kãriya ba daga barinta.
-
كَذَٰلِكَ وَقَدْ أَحَطْنَا بِمَا لَدَيْهِ خُبْرًا ٩١
Kazalika wa qad ahatna bima ladaihi khubra
Kamar wancan alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun kẽwaye da jarrabãwa ga abin da ke gunsa.
-
ثُمَّ أَتْبَعَ سَبَبًا ٩٢
Summa atba'a sababa
Sa'an nan kuma ya bi hanya.
-
حَتَّىٰ إِذَا بَلَغَ بَيْنَ السَّدَّيْنِ وَجَدَ مِن دُونِهِمَا قَوْمًا لَّا يَكَادُونَ يَفْقَهُونَ قَوْلًا ٩٣
Hatta iza balagha bainas saddaini wajada min dunihima qaumal la yakaduna yafqahuna qaula
Har a lõkacin da ya isa a tsakãnin duwãtsu biyu, ya sãmi waɗansu mutãne daga gabãninsu. Ba su yi kusa su fahimci magana ba.
-
قَالُوا يَا ذَا الْقَرْنَيْنِ إِنَّ يَأْجُوجَ وَمَأْجُوجَ مُفْسِدُونَ فِي الْأَرْضِ فَهَلْ نَجْعَلُ لَكَ خَرْجًا عَلَىٰ أَن تَجْعَلَ بَيْنَنَا وَبَيْنَهُمْ سَدًّا ٩٤
Qalu ya zal Qarnaini inna Ya'juja wa Ma'juja mufsiduna fil ardi fa hal naj'alu laka kharjan 'ala an taj'ala bainana wa bainahum sadda
Suka ce: "Yã Zulƙarnaini! Lalle ne Yãjũja da Majũja mãsu ɓarna ne a cikin ƙasa. To, ko zã mu Sanya harãji sabõda kai, a kan ka sanya wani danni a tsakãninmu da tsakãninsu?"
-
قَالَ مَا مَكَّنِّي فِيهِ رَبِّي خَيْرٌ فَأَعِينُونِي بِقُوَّةٍ أَجْعَلْ بَيْنَكُمْ وَبَيْنَهُمْ رَدْمًا ٩٥
Qala ma makkanni fihi rabbi khairun fa a'inuni bi quwwatin aj'al bainakum wa bainahum radma
Ya ce: "Abin da Ubangijĩna Ya mallaka mini, a cikinsa yã fi zama alhẽri. Sai ku taimakeni da ƙarfi, in sanya babbar katanga a tsakãninku da tsakãninsu."
-
آتُونِي زُبَرَ الْحَدِيدِ ۖ حَتَّىٰ إِذَا سَاوَىٰ بَيْنَ الصَّدَفَيْنِ قَالَ انفُخُوا ۖ حَتَّىٰ إِذَا جَعَلَهُ نَارًا قَالَ آتُونِي أُفْرِغْ عَلَيْهِ قِطْرًا ٩٦
Atuni zubaral hadidi hatta iza sawa bainas sadafaini qalanfukhu hatta iza ja'alahu naran qala atuni ufrigh 'alaihi qitra
"Ku kãwo mini guntãyen baƙin ƙarfe". (Suka kai masa) har a lõkacin da ya daidaita a tsakãnin duwãtsun biyu (ya sanya wutã a cikin ƙarfen) ya ce: "Ku hũra (da zugãzugai)." Har a lõkacin da ya mayar da shi wutã, ya ce: "Ku kãwo mini gaci (narkakke) in zuba a kansa."
-
فَمَا اسْطَاعُوا أَن يَظْهَرُوهُ وَمَا اسْتَطَاعُوا لَهُ نَقْبًا ٩٧
Fa masta'u an yazharuhu wa mastata'u lahu naqba
Dõmin haka bã za su iya hawansa ba, kuma bã zã su iya hujẽwa gare shi ba.
-
قَالَ هَٰذَا رَحْمَةٌ مِّن رَّبِّي ۖ فَإِذَا جَاءَ وَعْدُ رَبِّي جَعَلَهُ دَكَّاءَ ۖ وَكَانَ وَعْدُ رَبِّي حَقًّا ٩٨
Qala haza rahmatum mir rabbi fa iza ja'a wa'du rabbi ja'alahu dakka'a wa kana wa'du rabbi haqqa
Ya ce: "Wannan wata rahama ce daga Ubangijĩna. Sai idan wa'adin Ubangijĩna ya zo, ya mayar da shi niƙaƙƙe. Kuma wa'adin Ubangijĩna ya kasance tabbatacce."
-
وَتَرَكْنَا بَعْضَهُمْ يَوْمَئِذٍ يَمُوجُ فِي بَعْضٍ ۖ وَنُفِخَ فِي الصُّورِ فَجَمَعْنَاهُمْ جَمْعًا ٩٩
Wa tarakna ba'dahum yauma'izin yamuju fi ba'din wa nufikha fis suri fa jama'nahum jam'a
Kuma Muka bar sãshensu a rãnar nan, yanã garwaya a cikin sãshe, kuma aka bũsa a cikin ƙaho sai muka tãra su, tãrãwa.
-
وَعَرَضْنَا جَهَنَّمَ يَوْمَئِذٍ لِّلْكَافِرِينَ عَرْضًا ١٠٠
Wa 'aradna jahannama yauma'izil lil kafirina 'arda
Kuma Muka gitta Jahannama, a rãnar nan ga kãfirai gittãwa.
-
الَّذِينَ كَانَتْ أَعْيُنُهُمْ فِي غِطَاءٍ عَن ذِكْرِي وَكَانُوا لَا يَسْتَطِيعُونَ سَمْعًا ١٠١
Allazina kanat a'yunuhum fi ghita'in 'an zikri wa kanu la yastati'una sam'a
Waɗanda idãnunsu suka kasance a cikin rufi daga tunã Ni, kuma sun kasance bã su iya saurãrãwa.
-
أَفَحَسِبَ الَّذِينَ كَفَرُوا أَن يَتَّخِذُوا عِبَادِي مِن دُونِي أَوْلِيَاءَ ۚ إِنَّا أَعْتَدْنَا جَهَنَّمَ لِلْكَافِرِينَ نُزُلًا ١٠٢
Afahasibal lazina kafaru an yattakhizu 'ibadi min duni auliya'a inna a'tadna jahannama lil kafirina nuzula
Shin fa, waɗanda suka kãfirta sun yi zaton (daidai ne) su riƙi waɗansu bãyĩNa, majiɓinta baic iNa? Lalle ne, Mun yi tattalin Jahannama ta zama liyãfa ga kãfirai.
-
قُلْ هَلْ نُنَبِّئُكُم بِالْأَخْسَرِينَ أَعْمَالًا ١٠٣
Qul hal nunabbi'ukum bil akhsarina a'mala
Ka ce: "Kõ mu gaya muku game da mafĩfita hasãra ga ayyuka?"
-
الَّذِينَ ضَلَّ سَعْيُهُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَهُمْ يَحْسَبُونَ أَنَّهُمْ يُحْسِنُونَ صُنْعًا ١٠٤
Allazina dalla sa'yuhum fil hayatid dunya wa hum yahsabuna annahum yuhsinuna sun'a
"Waɗanda aikinsu ya ɓace a cikin rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sunã zaton lalle ne sũ, sunã kyautata, (abin da suke gani) aikin ƙwarai?"
-
أُولَٰئِكَ الَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِ رَبِّهِمْ وَلِقَائِهِ فَحَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ فَلَا نُقِيمُ لَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَزْنًا ١٠٥
Ula'ikal lazina kafaru bi ayati rabbihim wa liqa'ihi fa habitat a'maluhum fa la nuqimu lahum yaumal qiyamati wazna
Waɗancan ne waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Ubangijinsu, da kuma haɗuwa da Shi, sai ayyukansu suka ɓãci. Sabõda haka bã zã Mu tsayar musu da awo ba a Rãnar ¡iyãma.
-
ذَٰلِكَ جَزَاؤُهُمْ جَهَنَّمُ بِمَا كَفَرُوا وَاتَّخَذُوا آيَاتِي وَرُسُلِي هُزُوًا ١٠٦
Zalika jaza'uhum jahannamu bima kafaru wattakhazu ayati wa rusuli huzuwa
Wancan ne sakamakonsu shĩ ne Jahannama, sabõda kãfircinsu, kuma suka riƙi ãyõyi Na da Manzanni Na abin izgili.
-
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ كَانَتْ لَهُمْ جَنَّاتُ الْفِرْدَوْسِ نُزُلًا ١٠٧
Innal lazina amanu wa 'amilus salihati kanat lahum jannatul firdausi nuzula
Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Aljannar Firdausi ta kasance ita ce liyãfa a gare su.
-
خَالِدِينَ فِيهَا لَا يَبْغُونَ عَنْهَا حِوَلًا ١٠٨
Khalidina fiha la yabghuna 'anha hiwala
Suna madawwama a cikinta, bã su nẽman makarkata daga barinta.
-
قُل لَّوْ كَانَ الْبَحْرُ مِدَادًا لِّكَلِمَاتِ رَبِّي لَنَفِدَ الْبَحْرُ قَبْلَ أَن تَنفَدَ كَلِمَاتُ رَبِّي وَلَوْ جِئْنَا بِمِثْلِهِ مَدَدًا ١٠٩
Qul lau kanal bahru midadal li kalimati rabbi la nafidal bahru qabla an tanfada kalimatu rabbi wa lau ji'na bi mislihi madada
Ka ce: "Dã tẽku ta kasance tawada ga (rubũtun) kalmõmin Ubangijina, lalle ne dã tẽkun ta ƙãre a gabãnin kalmõmin Ubangijĩna su ƙãre, kuma kõda mun jẽ da misãlinsa dõmin ƙari."
-
قُلْ إِنَّمَا أَنَا بَشَرٌ مِّثْلُكُمْ يُوحَىٰ إِلَيَّ أَنَّمَا إِلَٰهُكُمْ إِلَٰهٌ وَاحِدٌ ۖ
Qul innama ana basharum mislukum yuha ilayya annama ilahukum ilahun wahid
Ka ce: "Nĩ, mutum ne kawai kamarku, anã yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lalle ne, Abin bautawarku, Abin bautawa Guda ne,
-
فَمَن كَانَ يَرْجُو لِقَاءَ رَبِّهِ فَلْيَعْمَلْ عَمَلًا صَالِحًا وَلَا يُشْرِكْ بِعِبَادَةِ رَبِّهِ أَحَدًا ١١٠
Fa man kana yarju liqa'a rabbihi falya'mal 'amalan salihan wa la yushrik bi 'ibadati rabbihi ahada
sabõda haka wanda ya kasance yanã fãtan haɗuwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na ƙwarai. Kuma kada ya haɗa kõwa ga bauta wa Ubangijinsa."
Alƙur'ani 18:1-110 · Falala: Hakim 2/368 (sahihi, Albani) · Daga Abu Sa'id al-Khudri: “Wanda ya karanta Suratul Kahf a ranar Juma'a, haske zai haskaka masa tsakanin Juma'a biyu.” Albani ya ce sahihi ne (Sahihul Jami' 6470); Ibn Hajar ya ce ita ce ruwaya mafi ƙarfi game da Suratul Kahf. Wasu suna ruwaito ta a matsayin maganar Abu Sa'id da kansa, da “daren Juma'a” (Darimi), kuma irin wannan lada ba a faɗar ta da ra'ayi, don haka tana da hukuncin maganar Annabi ﷺ; saboda haka ana karanta ta daga Magaribar Alhamis har zuwa Magaribar Juma'a. Ayoyinta goma na farko suna kare mutum daga Dujal (Muslim 809).