Hausa
Buɗe manhaja

Suratul Mulk: cikakken rubutu da tushe

Suratul Mulk (Tabarak), ayoyi talatin da ke yin ceto ga wanda ya karanta su, jumla bayan jumla: Larabci, karatu da boko da ma'ana.

Suratul Mulk

Mulki (Alƙur'ani 67)

Ayoyi talatin ne da suka yi wa wani mutum ceto har aka gafarta masa.

  1. بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ

    Bismillahir rahmanir rahim

    Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

  2. تَبَارَكَ الَّذِي بِيَدِهِ الْمُلْكُ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ ١

    Tabarakal lazi bi yadihil mulku wa huwa 'ala kulli shai'in qadir

    (Allah), Wanda gudãnar da mulki yake ga hannun Sa, Ya tsarkaka, kuma Shi Mai ĩko ne a kan kome.

  3. الَّذِي خَلَقَ الْمَوْتَ وَالْحَيَاةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا ۚ

    Allazi khalaqal mauta wal hayata li yabluwakum ayyukum ahsanu 'amala

    Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga cikinku ya fi kyãwon aiki,

  4. وَهُوَ الْعَزِيزُ الْغَفُورُ ٢

    Wa huwal 'azizul ghafur

    Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara.

  5. الَّذِي خَلَقَ سَبْعَ سَمَاوَاتٍ طِبَاقًا ۖ

    Allazi khalaqa sab'a samawatin tibaqa

    Shi ne wanda Ya halitta sammai bakawi, ɗabaƙõƙi a kan jũna,

  6. مَّا تَرَىٰ فِي خَلْقِ الرَّحْمَٰنِ مِن تَفَاوُتٍ ۖ

    Ma tara fi khalqir rahmani min tafawut

    bã za ka ga goggociya ba a cikin halittar (Allah) Mai rahama.

  7. فَارْجِعِ الْبَصَرَ هَلْ تَرَىٰ مِن فُطُورٍ ٣

    Farji'il basara hal tara min futur

    Ka sãke dũbawa, ko za ka ga wata ɓaraka?

  8. ثُمَّ ارْجِعِ الْبَصَرَ كَرَّتَيْنِ

    Summarji'il basara karratain

    Sa'an nan ka sake maimaita, dũbãwa,

  9. يَنقَلِبْ إِلَيْكَ الْبَصَرُ خَاسِئًا وَهُوَ حَسِيرٌ ٤

    Yanqalib ilaikal basaru khasi'au wa huwa hasir

    ganinka zai komo maka, gajiyayye, ba da ganin wata naƙasa bã.

  10. وَلَقَدْ زَيَّنَّا السَّمَاءَ الدُّنْيَا بِمَصَابِيحَ

    Wa laqad zayyannas sama'ad dunya bi masabih

    Kuma lalle Mun ƙawãta samar farko da fitillu,

  11. وَجَعَلْنَاهَا رُجُومًا لِّلشَّيَاطِينِ ۖ

    Wa ja'alnaha rujumal lish shayatin

    kuma Muka sanya su abin jifa ga shaiɗanu,

  12. وَأَعْتَدْنَا لَهُمْ عَذَابَ السَّعِيرِ ٥

    Wa a'tadna lahum 'azabas sa'ir

    kuma Muka yi musu tattalin azãbar Sa'ĩr.

  13. وَلِلَّذِينَ كَفَرُوا بِرَبِّهِمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ ۖ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ ٦

    Wa lil lazina kafaru bi rabbihim 'azabu jahannam, wa bi'sal masir

    Kuma waɗanda suka kafirce wa Ubangjinsu na da azãbar Jahannama, tã munana ga zamanta makõmarsu.

  14. إِذَا أُلْقُوا فِيهَا سَمِعُوا لَهَا شَهِيقًا وَهِيَ تَفُورُ ٧

    Iza ulqu fiha sami'u laha shahiqau wa hiya tafur

    Idan an jẽfa su a cikinta, sai su ji daga gare ta wata ƙãra, tana tafasa.

  15. تَكَادُ تَمَيَّزُ مِنَ الْغَيْظِ ۖ

    Takadu tamayyazu minal ghaiz

    Tana kusa ta tsãge domin hushi,

  16. كُلَّمَا أُلْقِيَ فِيهَا فَوْجٌ سَأَلَهُمْ خَزَنَتُهَا أَلَمْ يَأْتِكُمْ نَذِيرٌ ٨

    Kullama ulqiya fiha faujun sa'alahum khazanatuha alam ya'tikum nazir

    ko da yaushe aka jẽfa wani ɓangaren jama'a a cikinta, matsaranta na tambayar su da cewa, "Wani mai gargaɗi bai je muku ba?"

  17. قَالُوا بَلَىٰ قَدْ جَاءَنَا نَذِيرٌ فَكَذَّبْنَا

    Qalu bala qad ja'ana nazirun fa kazzabna

    Sai su ce: "I, lalle wani mai gargaɗi ya je mana, sai muka ƙaryata shi,

  18. وَقُلْنَا مَا نَزَّلَ اللَّهُ مِن شَيْءٍ

    Wa qulna ma nazzalallahu min shai'

    muka ce, 'Allah bai saukar da kome ba,

  19. إِنْ أَنتُمْ إِلَّا فِي ضَلَالٍ كَبِيرٍ ٩

    In antum illa fi dalalin kabir

    bã ku cikin kõme sai ɓata babba.'"

  20. وَقَالُوا لَوْ كُنَّا نَسْمَعُ أَوْ نَعْقِلُ مَا كُنَّا فِي أَصْحَابِ السَّعِيرِ ١٠

    Wa qalu lau kunna nasma'u au na'qilu ma kunna fi ashabis sa'ir

    Kuma suka ce: "Dã mun zamo muna saurãre, kõ muna da hankali, dã ba mu kasance a cikin 'yan sa'ĩr ba."

  21. فَاعْتَرَفُوا بِذَنبِهِمْ فَسُحْقًا لِّأَصْحَابِ السَّعِيرِ ١١

    Fa'tarafu bi zanbihim fa suhqal li ashabis sa'ir

    Wato su yi iƙrãri da laifinsu. Allah Ya la'ani'yan sa'ĩr!

  22. إِنَّ الَّذِينَ يَخْشَوْنَ رَبَّهُم بِالْغَيْبِ

    Innal lazina yakhshauna rabbahum bil ghaib

    Lalle waɗanda ke tsõron Ubangjinsu, a ɓoye,

  23. لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ كَبِيرٌ ١٢

    Lahum maghfiratuw wa ajrun kabir

    suna da wata gãfara da wani sakamako mai girma.

  24. وَأَسِرُّوا قَوْلَكُمْ أَوِ اجْهَرُوا بِهِ ۖ

    Wa asirru qaulakum awijharu bih

    Kuma ku asirta maganarku ko ku bayyana ta,

  25. إِنَّهُ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ ١٣

    Innahu 'alimum bi zatis sudur

    lalle shi, (Allah), Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza.

  26. أَلَا يَعْلَمُ مَنْ خَلَقَ وَهُوَ اللَّطِيفُ الْخَبِيرُ ١٤

    Ala ya'lamu man khalaq, wa huwal latiful khabir

    Ashe, wanda Ya yi halitta bã zai iya saninta ba, alhãli kuwa shi Mai tausasãwa ne, kuma Mai labartawa?

  27. هُوَ الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ الْأَرْضَ ذَلُولًا

    Huwal lazi ja'ala lakumul arda zalula

    Shi, (Allah), Yã sanya muku ƙasa hõrarriya,

  28. فَامْشُوا فِي مَنَاكِبِهَا وَكُلُوا مِن رِّزْقِهِ ۖ

    Famshu fi manakibiha wa kulu mir rizqih

    sai ku tafi cikin sãsanninta, kuma ku ci daga arzikin Sa,

  29. وَإِلَيْهِ النُّشُورُ ١٥

    Wa ilaihin nushur

    kuma zuwa gare shi ne tãshin yake.

  30. أَأَمِنتُم مَّن فِي السَّمَاءِ

    A'amintum man fis sama'

    Shin kõ kun amince cewa wanda ke cikin sama,

  31. أَن يَخْسِفَ بِكُمُ الْأَرْضَ فَإِذَا هِيَ تَمُورُ ١٦

    Ay yakhsifa bikumul arda fa iza hiya tamur

    bã zai iya shãfe ƙasa tãre da ku ba, sai ga ta tana mai girgiza?

  32. أَمْ أَمِنتُم مَّن فِي السَّمَاءِ أَن يُرْسِلَ عَلَيْكُمْ حَاصِبًا ۖ

    Am amintum man fis sama'i ai yursila 'alaikum hasiba

    Kõ kun amincẽ cewa wanda ke cikin sama bã zai iya sako muku iskar gũguwa ba?

  33. فَسَتَعْلَمُونَ كَيْفَ نَذِيرِ ١٧

    Fa sata'lamuna kaifa nazir

    To, zã ku san yadda (ãƙibar) gargaɗi Na take.

  34. وَلَقَدْ كَذَّبَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ فَكَيْفَ كَانَ نَكِيرِ ١٨

    Wa laqad kazzabal lazina min qablihim fa kaifa kana nakir

    Lalle, waɗanda ke gabansu sun ƙaryata (manzanni). To, yãya (ãƙibar) gargaɗi Na ta kasance?

  35. أَوَلَمْ يَرَوْا إِلَى الطَّيْرِ فَوْقَهُمْ صَافَّاتٍ وَيَقْبِضْنَ ۚ

    Awa lam yarau ilat tairi fauqahum saffatiw wa yaqbidn

    Bã zã su yi dũbi ba zuwa ga tsuntsãye a kansu, mãsu sanwã, kuma suna fiffikãwa,

  36. مَا يُمْسِكُهُنَّ إِلَّا الرَّحْمَٰنُ ۚ

    Ma yumsikuhunna illar rahman

    bãbu mai riƙe da su sai (Allah), Mairahama?

  37. إِنَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ بَصِيرٌ ١٩

    Innahu bi kulli shai'in basir

    Lalle shi Mai gani ne ga dukan kõme.

  38. أَمَّنْ هَٰذَا الَّذِي هُوَ جُندٌ لَّكُمْ يَنصُرُكُم مِّن دُونِ الرَّحْمَٰنِ ۚ

    Amman hazal lazi huwa jundul lakum yansurukum min dunir rahman

    Wãne ne wanda zai zame muku mayãƙin da zai taimake ku, wanda bã (Allah) ba, Mai rahama?

  39. إِنِ الْكَافِرُونَ إِلَّا فِي غُرُورٍ ٢٠

    Inil kafiruna illa fi ghurur

    Kãfirai ba su a cikin kõme fãce rũɗu.

  40. أَمَّنْ هَٰذَا الَّذِي يَرْزُقُكُمْ إِنْ أَمْسَكَ رِزْقَهُ ۚ

    Amman hazal lazi yarzuqukum in amsaka rizqah

    Wãne ne wanda zai ciyar da ku, idan (Allah) Ya riƙe arzikin Sa?

  41. بَل لَّجُّوا فِي عُتُوٍّ وَنُفُورٍ ٢١

    Bal lajju fi 'utuwwiw wa nufur

    A'aha, sun yi zurfi cikin girman kai da tãshin hankali.

  42. أَفَمَن يَمْشِي مُكِبًّا عَلَىٰ وَجْهِهِ أَهْدَىٰ

    Afamai yamshi mukibban 'ala wajhihi ahda

    Shin, wanda ke tafiya a kife a kan fuskarsa yã fi zama a kan shiryuwa,

  43. أَمَّن يَمْشِي سَوِيًّا عَلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ ٢٢

    Ammai yamshi sawiyyan 'ala siratim mustaqim

    ko kuwa wanda ke tafiya miƙe a kan hanya madaidaiciya?

  44. قُلْ هُوَ الَّذِي أَنشَأَكُمْ

    Qul huwal lazi ansha'akum

    Ka ce: "(Allah) Shine Wanda Ya ƙaga halittarku,

  45. وَجَعَلَ لَكُمُ السَّمْعَ وَالْأَبْصَارَ وَالْأَفْئِدَةَ ۖ

    Wa ja'ala lakumus sam'a wal absara wal af'idah

    Ya sanya muku ji da gani da tunãni,

  46. قَلِيلًا مَّا تَشْكُرُونَ ٢٣

    Qalilam ma tashkurun

    amman kaɗan ce ƙwarai godiyarku!"

  47. قُلْ هُوَ الَّذِي ذَرَأَكُمْ فِي الْأَرْضِ وَإِلَيْهِ تُحْشَرُونَ ٢٤

    Qul huwal lazi zara'akum fil ardi wa ilaihi tuhsharun

    Kuma kace "Shi ne Ya halitta ku daga ƙasã, kuma zuwa gare Shi ne ake tãshin ku."

  48. وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا الْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ ٢٥

    Wa yaquluna mata hazal wa'du in kuntum sadiqin

    Kuma sunã cewa, "Yaushe ne wannan alkawarin zai tabbata in dai kun kasance mãsu gaskiya ne kũ?"

  49. قُلْ إِنَّمَا الْعِلْمُ عِندَ اللَّهِ وَإِنَّمَا أَنَا نَذِيرٌ مُّبِينٌ ٢٦

    Qul innamal 'ilmu 'indallahi wa innama ana nazirum mubin

    Ka ce: "Ilmin a wurin Allah kawai yake, kuma ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyana (gargaɗin)."

  50. فَلَمَّا رَأَوْهُ زُلْفَةً سِيئَتْ وُجُوهُ الَّذِينَ كَفَرُوا

    Fa lamma ra'auhu zulfatan si'at wujuhul lazina kafaru

    To, lokacin da suka gan ta (azãbar) a kusa, fuskokin waɗanda suka kãfirta suka mũnana,

  51. وَقِيلَ هَٰذَا الَّذِي كُنتُم بِهِ تَدَّعُونَ ٢٧

    Wa qila hazal lazi kuntum bihi tadda'un

    kuma aka ce (musu) wannan shi ne abin da kuka zamo kuna ƙaryatãwa.

  52. قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِنْ أَهْلَكَنِيَ اللَّهُ وَمَن مَّعِيَ أَوْ رَحِمَنَا

    Qul ara'aitum in ahlakaniyallahu wa mam ma'iya au rahimana

    Ka ce musu "Idan Allah Ya halaka ni nĩ da wanda ke tãre da ni, ko kuma, Yã yi mana rahama,

  53. فَمَن يُجِيرُ الْكَافِرِينَ مِنْ عَذَابٍ أَلِيمٍ ٢٨

    Fa mai yujirul kafirina min 'azabin alim

    to, wãne ne zai tserar da kafirai daga wata azãba mai raɗaɗi?"

  54. قُلْ هُوَ الرَّحْمَٰنُ آمَنَّا بِهِ وَعَلَيْهِ تَوَكَّلْنَا ۖ

    Qul huwar rahmanu amanna bihi wa 'alaihi tawakkalna

    Ka ce: "Shĩ ne Mai rahama mun yi ĩmãni da Shi, gare Shi muka dogara,

  55. فَسَتَعْلَمُونَ مَنْ هُوَ فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ ٢٩

    Fa sata'lamuna man huwa fi dalalim mubin

    saboda haka zã ku san wanda yake a cikin ɓata bayyananniya."

  56. قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِنْ أَصْبَحَ مَاؤُكُمْ غَوْرًا

    Qul ara'aitum in asbaha ma'ukum ghaura

    Ka ce: "Ko kun gani, idan ruwanku ya wãyi gari faƙaƙƙe,

  57. فَمَن يَأْتِيكُم بِمَاءٍ مَّعِينٍ ٣٠

    Fa mai ya'tikum bi ma'im ma'in

    to, wãne ne zai zo muku da ruwa wani mai ɓuɓɓuga?"

Alƙur'ani 67:1-30 · Falala: Tirmizi 2891 (hasan, Albani), Abu Dawud 1400 (hasan, Albani) · Ayoyi talatin ne da suka yi wa wani mutum ceto har aka gafarta masa (Tirmizi 2891). Cewa Annabi ﷺ ba ya barci sai ya karanta as-Sajdah da Tabarak yana cikin Tirmizi 2892, kuma malamai sun yi saɓani a kansa (sahihi a wurin Albani; mai rauni (da'ifi) a wurin Darussalam).